
Tsohon Gwamnan Jigawa, Sule Lamido yayi barzanar Kai jami’iyyarsa ta PDP kara kotu.
Sule Lamido ya bayyana hakane bayan kasa sayen Fom din tsayawa takarar shugaban jam’iyyar a ranar Litinin
Yace idan bai samu damar sayar fom din ba zai iya garzayawa kotu dan jin dalilin da yasa aka hanashi.
A baya dai, Sule Lamido ya bayyana aniyarsa ta son tsayawa takarar shugaban jam’iyyar PDP a shafinsa na Facebook.
Saidai wasu manya a jam’iyyar sun bayyana cewa, Kabiru Tanimu Turaki suke son tsayarwa a matsayin shugaban jam’iyyar