
Shugaban ƙasar Kamaru mai shekara 92 a duniya ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasar a karo na takwas, bayan da Majalisar Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen na ranar 12 ga watan Oktoba.
Biya ya lashe zaɓen ne bayan ya samu kashi 53.66% na ƙuri’un da aka kaɗa, yayin da babban abokin hamayyarsa Issa Tchiroma Bakary ya zo na biyu da kashi 35.19%, kamar yadda Majalisar ta bayyana.
“Paul Biya ya zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, bayan ya samu mafi yawa na ƙuri’un da aka kaɗa,” in ji Clement Aatanga, shugaban Majalisar Kundin Tsarin Mulki ta ƙasar.
Kashi 57.76% ne na waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri’a suka fita domin yin zaɓen, inda kashi 42.24% suka ƙaurace.