
Me martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa dama ba abin mamaki bane dan an samu hauhawar farashin kayan abinci da tsadar rayuwa bayan cire tallafin man fetur.
Yace dama hakan dole zata faru.
Yace babban abin dubawa shine abinda zai faru da ba’a cire tallafin man fetur din ba.
Ya bayyana hakane a wajan wani taro inda jawabinsa na wajan taron ke ta yaduwa a kafafen sadarwa.
Yace bashi ake ciyowa ana biyan kudin tallafin sanan akwai kudin ruwa da ake biya akan bashin.
Da yake magana kan irin shuwagabannin da ake dasu a Najeriya, yace yana mamakin ace mutum me ilimi amma ya zama da koron siyasa, hakanan yana mamakin shugaba da ba zai saurari suka daga na kusa dashi ba dan ya gyara inda yake da matsala.
Sarki Sanusi yace ko da an cire ‘yan majalisar Najeriya aka sake zuba wasu, ba lallai a ga canji ba, saboda gasunan da ilimi amma suna irin abubuwan Jahilai.