
Tauraron fina-finan Hausa kuma dan Tiktok Bana ya fito ya baiwa masoyansa da ‘yan uwa hakuri bayan Bidiyon da ya saki yana sukar A’isha Humaira da mijinta Rarara.
Saidai jim kadan bayan sakin Bidiyon sai ga Bana ya sake sakin wani Bidiyon yana cewa, ya koma gida ya iske an aika masa wasu tsagera.
Yace dai ko me ya sameshi su za’a kama.
Tun Farko dai Bana ya wallafa Bidiyon inda ya soki Rarara game da wani Bidiyo da yayi zargin cewa Rarara din ya kama kugun wata Amarya.
Lamarin dai ya jawo cece-kuce sosai inda har sai da A’isha Humaira ta ce masa ya goge Bidiyon sannan ya bada hakuri nan da sati daya ko zata makashi kara kotu.