
Hukumar bayar da agaji ta kasa, NEMA ta karbi ‘yan Najeriya 131 da suka fito daga kasar Nijar wanda aka dawo dasu bisa son ransu.
Mutanen sun je Chirani ne kuma an dukosu daga garin Agadez, Niger Republic zuwa Najeriya.
Hukumar tace ranar Alhamis, 30th October, 2025 ne aka dawo da ‘yan Najeriya a filim Malam Aminu Kano dake Kano.
Hukumar kula da shige da fici ta kasa, NIS ta dauki bayanan mutanen da aka dawo dasu din inda kuma aka basu abubuwan kula kamar abinci da sauransu.