
Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo ya bayyana cewa, a yankinsa na kudu maso gabas na Inyamurai wadanda kaso 95 cikin 100 Kiristoci ne, masu Khashye mutanensu kiristoci ne.
Ya bayyana hakane a wajan wani taro da aka gudanar Ranar Lahadi inda yake martani kan zargin Khisan Khiyashi da aka ce anawa kiristoci a Najeriya.
Ya bayyana cewa dan haka maganar ta wuce ta addini.
Yace kuma Gwamnatin Najeriya na iya bakin kokarinta wajan shawo kan matsalar tsaron.
Sannan ya bayyana fatan nan gaba kasar zata magance wannan matsala ba tare da wani haufi ba.