
Sanata A’ishatu Dukku ta bayyana cewa bata san dalilin da yasa mutanen Najeriya suka canja ba, tace ko da saboda magin da ake sha ne?
Tace Bafulatani Allah ya halicceshi ne shi yana son Saniyarsa fiye da yanda yake son kansa bama wai wani ba.
Ta bayyana hakane a zauren majalisar Dattijai yayin da ake tattauna maganar hare-haren da Fulani Makiyaya ke kaiwa manoma.