
Babban Malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa, ko kasar Amurka ta zo Najeriya ba zata iya magance matsalar tsaron Najeriya ba.
Malam ya bayyana cewa da kasar Rasha ko China ne suka ce zasu kawowa Najeriya dauki za’a yadda dasu saboda a baya basu yiwa kasashe katsalandan a harkokin su na cikin gida.
Yace amma America ba da gaske take ba.
Yace kuma tunda sojojin Najeriya suka kasa magance matsalar, suma sojojin Amurka ko sun zo ba zasu iya magance matsalar ba.