Rahotanni da bidiyo sun yo ta yawo kan Yadda Kanawa suka yiwa Gwamna Abba Kabir ihun bamayi a hanyarsa ta zuwa sallar Idi.
Lamarin bai zo da mamaki ba ganin lamuran da suka faru a jihar ta Kano daga Chanja sarki wanda baiwa masu son Aminu Ado Bayero dadi ba zuwa rusau.
An yi rusau din shaguna da yawa ana kwanaki 4 kamin Sallah a IBB wanda har ya jawo Wasu ‘yan kasuwar suka yi zanga-zanga.
Wannan dai ka iya zamarwa gwamnatin Abba Kabir Yusuf kalubale.