Friday, December 5
Shadow

Gwamnatin tarayya na rokon kasar Ingila ta bada dama a dawo da Sanata Ike Ekweremadu ya ci gaba da zaman gidan yarinsa a Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta fara rokon gwamnatin ingila ta taimaka a dawo da sanata Ike Ekweremadu Najeriya ya ci gaba da zaman gidan yarinsa anan.

A jiyane Hutudole ya kawo muku cewa, Shugaba Tinubu ya aike da wata tawaga ta musamman zuwa kasar Ingima dan kaiwa Sanata Ike Ekweremadu ziyara a gidan yarin da yake daure acan.

Saidai Sabbin Rahotanni daga Daily Trust sun bayyana cewa, Gwamnati ta aika wakilanne zuwa Ingila dan su roki hukumomin kasar su bayar da dama a dawo da Sanata Ekweremadu zuwa Najeriya ya ci gaba da zaman gidan yarinsa anan.

Rahoton yace Wakilan Gwamnatin Najeriyar na kuma rokon a sassautawa Sanata Ekweremadu hukunci ko kuma a rage yawan shekarun da aka yanka masa na zama a gidan yarin.

Karanta Wannan  Gwamnatin tarayya tace zata rama tsaurara Yin Bizar da kasar Amurka ta kakabawa 'yan Najeriya

An yankewa Sanata Ike Ekweremadu hukuncin daurin shekaru 9 a gidan yarin kasar Ingila bayan samunsa da hannu a safarar sassan jikin dan Adam.

Wakilan Gwamnatin Najeriyar da suka je kasar ta Ingila sune Ministan Harkokin kasashen waje, Yusuf Maitama Tuggar, sai kuma Babban Lauyan Gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *