
Tsohon Shugaban sojojin Najeriya, Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa, zagin da Ministan Abuja, Nyesom Wike yawa matashin soja da ya hanashi shiga wani Fili dan ya rusashi cin fuskane.
Buratai yace dolene a rika girmamawa da kuma sanya jami’an soji a gaba a kasarnan.
Yace tsaro shine ke zuwa farko kuma zagin da Wike yawa matashin sojan cin fuskane da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da Sojan da hukumar sojojin Najeriya.
Buratai yace dolene Wike ya fito ya baiwa matashin sojan hakuri, da shugaba Tinubu, dama Hukumar soji.
Yayi kira ga shugaba Tinubu da ya dauki matakin da ya dace akan lamarin.
Wike dai ya zagi wani matashin soja ne da ya hanashi shiga wani fili wanda na sojoji ne dan hana ci gaba da gini a filin, sojan yace an bashi umarnine.