
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayar da tabbacin cewa, Najeriya zata fita daga Talaucin da take fama dashi.
Ya bayyana hakane ranar Laraba a wajan taron kungiyar mawallafa jaridu ta Najeriya.
Yace lallai Najeriya na fama da talauci amma kuma ba zata kasance cikin Talauci ba nan da shekaru masu zuwa.
Shugaban ya bayyana cewa, Gyare-Gyaren da ya dauko suna da tsauri da wahala amma ya daukosu ne da gyaran Tattalin Arzikin Najeriya.