
Wani dan Arewa dake zaune a kudancin Najeriya ya tsinci wayar iPhone 13 promax ya mayarwa da mai ita.
Mutumin sunansa Sulaiman, ya bi sahun matar ya mayar mata da wayarta.
Matar tace ta hau Keke Napep ne ta yadda wayar tata inda bayan da mutumin ya mayar mata da wayar ta rika rungumarsa tana murna tana gode masa.