
Rahotanni sun bayyana cewa, Kiristoci 104 ne suka karbi Musulunci a wani kauye na jihar Delta dake kudancin Najeriya.
Hakan na zuwane yayin da ake yada rade-radin cewa ana yiwa Kiristoci kisan Khiyashi a Kasarnan wanda har aka gayyato kasar Amurka ta kawo musu dauki.