
Kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa baya jin dadin abinda ke faruwana kasarnan.
Yace Gwamnatin tarayya ce ke da alhakin samar da tsaro a kasarnan, babu wani bako daga kasar waje da zai zo ya iya samar da tsaro a Najeriya.
Akpabio ya bayyana hakane a Jos yayin karbar wasu mutane da suka koma jam’iyyar APC.
Yace yana fatan Allah ya taimakesu su da suke tare da gwamnatin tarayya su samu su sauke nauyin dake kansu na son kawo zaman Lafiya a jihar Filato.