
Dan takarar shugaban kasa kuma mawallafin jaridar Sahara reporters sannan dan fafutuka, Omoyele Sowore ya ce dole ne a saki Sheikh Abduljabbar.
Ya bayyana hakane a shafinsa na X inda yace rashin adalci ne ci gaba da tsare malam Abduljabbar.
Malam Abduljabbar na fuskantar hukunci ne bayan samunsa da laifin yin batanci ga Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam).
A baya, Sowore yayi fafutuka dan neman ganin an saki wasu da ake tsare dasu da dama.