
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF tace tana baiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da sauran ‘yan Najeriya hakuri saboda fitar da Super Eagles da kasar Dr. Congo ta yi a wasan neman cancantar zuwa buga gasar cin kofin Duniya na shekarar 2026.
NFF tace lamarin abin takaicine matuka domin sau biyu kenan a jere tana kasa zuwa gasar.
Tace abin kunya ne amma tana neman afuwa.
Kasar Dr. Congo tawa Najeriya ci 4-3 bayan an tashi 1-1 a jiya Lahadi wanda hakan ya hana Najeriya damar kaiwa ga gasar cin kofin Duniya na shekarar 2026.