Saturday, June 27
Shadow

Da Duminsa: Dan gidan tsohon shugaban kasa, IBB Muhammad Babangida yace ba gaskiya bane cewa wai yaki amincewa da mukamin da shugaba Tinubu ya bashi, yace ya amince

Dan gidan tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, IBB me suna Muhammad Babangida yace ya amince da mukamin da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya nadashi.

Ya musanta rahotannin dake cewa bai amince da nadin mukamin ba.

A ranar 18 ga watan Yuli ne shugabab kasa, Bola Ahmad Tinubu ya nada Muhammad Babangida mukamin shugaban bankin Noma BAO.

A sanarwar da ya fitar, me taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkar sada zumunta, Dada Olusegun yace Muhammad Babangida ya fitar da sanarwa a yau Litinin inda yace ya amince da mukamin da shugaba Tinubu ya nadashi.

Muhammad Babangida yace masu cewa wai bai amince ba na son bata gwamnatin Tinubu ne kawai.

Karanta Wannan  DA DUMI DUMI: Rahotanni Sun tabbatar da cewa Ganduje ya shiga É—imuwa yakasa zaune yakasa tsaye Bisa jin cewar Kwankwaso Zai shiga cikin jam'iyyar Apc, An shiga fargaba a APC kan batun dawowar Kwankwaso jam'iyyar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *