
Kafar yada labarai ta BBC bangaren Turanci na shan suka saboda karyar da suka yi a rahoton da duka wallafa game da garkuwa da dalibai ‘yan mata na jihar Kebbi.
BBC ta bayyana a rahoton cewa, an yi musayar wuta ne da ‘yan Bindigar da suka yi garkuwa da daliban.
Saidai da yawa sun bayyana cewa labarin ba haka yace ba, ‘yan Bindigar sun yi harbe-harbe ne kamin sace daliban.
Har kafar X da suka wallafa labarin akai ma ta karyata wannan ikirarin na BBC.