
Wata kungiya me suna The Global Coalition for Security and Democracy in Nigeria ta ‘yan Najeriya wadda suka kafa a kasar Amirka tace ta yi na’am da Amurka ta saka Najeriya cikin kasashen da zata rika sakawa ido.
Kumgiyar tace tana kira ga shugaban kasar Amurka, Donald Trump da ya gaggauta kawo Kharin da yace zai kawo Najeriya.
Kungiyar ta bayyana hakane a sanarwar data fitar ta bakin shugabanta, Comrade Frederick Odorige inda tace tana goyon karfafa tsaro da Dimokradiyya a Najeriya.