Friday, December 5
Shadow

Tinubu zai je Afirka ta Kudu da Angola

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai bar ƙasar a yau Laraba domin halartar taron G20 da taro tsakanin kungiyar Tarayyar Turai da ta Tarayyar Afirka.

‎Shugaban zai soma ziyarar ne a Johannesburg,babban birnin ƙasar Afrika ta kudu, inda zai halarci karo na ashirin na taron shugabannin ƙasashe ashirin masu ƙarfin tattalin arziƙi wato G20 a ranakun 22 da 23 ga watan Nuwamba.

Daga nan zai tafi birnin Luanda da ke Angola domin halartar taron kungiyar Tarayyar Turai da Tarayyar Afirka karo na 7 a ranakun 24 da 25 ga watan Nuwamban 2025.

Waɗannan bayanai na ƙunshe ne a cikin sanarwa da mai magana da yawun shugaban Bayo Onanuga ya fitar a babban birnin ƙasar Abuja, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

Karanta Wannan  Da Duminsa:Kotu ta kwace kujerar dan majalisar wakilai daga jihar Zamfara bayan da ya fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC

Ana kuma sa ran Shugaba Tinubu zai yi wasu ganawa a yayin taron domin bunkasa shirinsa na sabunta fata da kuma tattaunawa kan zaman lafiya da tsaro da kuma ci gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *