
Rahotanni daga jihar Naija na cewa, an sake yin garkuwa da dalibai na makatanta.
An sace daliban makarantar St. Mary’s School ce dake Papiri a karamar hukumar Agwara dake jihar ta Naija.
Daily Trust tace lamarin ya farune da misalin karfe 2 zuwa 3 na dare.
Zuwa yanzu dai ba’a san yawan daliban da aka sace ba.
Me magana da yawun gwamnatin jihar Naija, Abubakar Usman ya tabbatar da wannan labari inda yace ana kokarin kubutar da daliban.
Saidai ya dora laifin faruwar hakan akan hukumomin makarantar inda yace Gwamnati ta samu rahoton cewa, hakan zai iya faruwa.
Kuma ta bayar da sanarwa cewa, a kulle duka makarantu a yankin saidai wannan makaranta taki jin wannan shawara inda suka ci gaba da karatu.