
Hukumar ‘yansandan Najeriya ta fitar da bayanan gargadi inda take cewa, ‘yan Bindiga na ta kwarara zuwa jihar Kogi.
Tace hakan na faruwane saboda su gujewa luguden wuta da ake musu a jihohin Naija da Kwara.
Hakanan sanarwar wadda kafar Sahara reporters ta ce ta samo ta bayyana cewa, tshageran Dhajin na shirin kai hari kan makarantun Ochaja Boys and Girls Secondary Schools da kuma jami’ar Prince Abubakar Audu University, Anyigba, da bankuna da guraren Ibada da ofisoshin ‘yansanda.
Sanarwar tace tshageran Dhajin na dauke da muggan makamai masu hadarin gaske.