Tuesday, February 3
Shadow

Ya kamata ƴan Najeriya su sauya halayensu – Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci ƴan Najeriya da su sauya tunaninsu a kan kasa tasu.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa shugaban dai na magana ne yayin da ya karɓi baƙuncin tawaga daga majalisar dokokin ƙasar waɗanda suka kai masa ziyarar barka da sallah,.

Mista Tinubu ya ce “lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su sauya hali da tunaninsu ga Najeriya domin ciyar da ƙasar gaba”.

“Yan ƙasa da ke yawon neman wayar lantarki domin su cire da tuge titin dogo da dai sauran ayyukan ɓaagari, E, na amince akwai talauci, akwai wahalhalu. Amma ba mu kaɗai ne mutanen da muke shan wahala ba. Dole ne mu tunkari kalubalen da ke gabanmu.” In ji Tinubu.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Fasto da ya lura mata na zuwa cocinsa sanye da riga kawai babu rogar Mama a ciki ya raba musu rigar maman saidai yace ba zasu tafi da ita gida ba, da an gama zaman cocin su cire su aje mai kayansa

Ya ƙara da cewa “akwai bukatar wasu ƴan ƙasar su sauya tunaninsu su kuma zama masu taimakawa wajen warware ƙalubalen da tattalin arziƙin ƙasar ke fuskanta. Saboda haka akwai buƙatar daina fasaƙwauri da cin dunduniyar tattalin arziƙin.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *