
Wasu da ake zargin ‘yan Kungiyar ÌPÒB ne masu son kafa kasar Biafra a birnin Aba na jihar Abia, sun hallaka wani sojan Najeriya me suna David.
Sun hallaka sojan ne yayin da ya dauki hutu ya je gidan mahaifinsa dan ya gana dasu.
Sun hallakashi ne biyo bayan yankewa Nnamdy Khanu hukuncin daurin rai da rai da kotu tayi.
Hukumar sojojin Najeriya ta baiwa sojoji shawarar su rika kula da mutanen da suke tare dasu sannan idan ba a kungiyance suke ba, su daina saka kayan aiki su rika saka kayan gida.
