
Malamin Addinin Islama, Sheikh Isa Ali Pantami ya tabu sosai da rasuwar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.
Bayan Wallafa sakon ta’aziyya da yayi, ya kuma wallafa wani tsohon Bidiyon da suke tare da Dahiru Bauchi inda yaje gaisheshi.
A yau ne dai bayan Sallar Juma’a ake sa ran yiwa gawar Marigayin Sutura a kaishi makwancinsa.