
Tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa, Doka ta bayar da dama idan Gwamnatin tarayya ta gaza, ‘yan Najeriya zasu iya neman dauki daga kasashen waje kan matsalar tsaro.
Obasanjo yace a lokacin da yayi mulki yasan cewa, Najeriya na da karfin da zata iya magance matsalar tsaro.
Yayi kira ga Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu da ta tashi tsaye ta magance matsalar dake ci gaba da ruruwa a sassa daban-daban na kasarnan.