Zufar hammata bata da dadi inda idan ta yi yawa takan sa mutum ya rika wari wanda zai dameshi, ya kuma dami mutanen dake kusa dashi.
Dan hakane masu fama da zufar hammata ke neman hanyar kawar da ita.
Akwai hanyoyi da yawa na kawar da zufar hammata kuma ana iya samar dasu a gida ba tare da ganin likita ba.
Daya daga cikin hanyar magance matsalar zufar hamata itace a bari jiki ya bushe bayan an yi wanka kamin a saka kaya.
Masana kiwon lafiya sun ce hakan na da matukar tasiri wajan magance matsalar zufar hammata.
Aske Gashin Hamata: Aske Gashin hamata yana rage zufar hamatar da kuma warin da hamatar ke yi.
A daina cin abinci me sanya zufa, kalar abincin da ake ci na takmakawa wajan yawan zufar da ake fama da ita.
Abincin dake sanya zufa sun hada da:
Abinci me yaji
Tafarnuwa
Albasa
Ice cream.
Abincin Gwangwani dana Leda wadanda aka sarrafa.
Giya
Coffee da sauransu.
A rika cin abincin dake rage kiba.
Wadannan abincin sun hada da:
Ruwa
Ayaba.
Man Zaitun
Dankalin Hausa.
Kankana
Alkama da sauransu.
A rika shan ruwa sosai.
A daina saka kayan da suka matse a rika saka kaya wanda iska ke ratsasu.
A daina shan taba, sinadarin dake cikin taba na taimakawa wajan kara yawan zufa.