
Tsohon Babban lauyan Gwamnatin tarayya, Abubakar Malami wanda a jiya yace hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC sun gayyaceshi, yace bayan kammala masa tambayoyi, sun sakeshi.
Ga sakon da ya wallafa a shafinsa:
“Dangane da alkawarina na ci gaba da sanar da ’yan Najeriya game da gayyatar da EFCC ta yi mini, ina mika godiya ga Allah bisa bani ikon fitowa cikin aminci.
Tattaunawar ta kasance mai kyau, kuma na samu fitowa, haka zalika an sake sanya wani sabon lokaci domin ci gaba da tattaunawa yayin da gaskiyar da ta shafi ƙagaggun zarge-zargen da aka yi a kaina ke ci gaba da bayyana.
ABUBAKAR MALAMI, SAN, CON”