Saturday, June 27
Shadow

Da Duminsa: Abin ya zo, Kasar Amurka ta turo jirgin Leken Asiri Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa, Kasar Amurka ta aiko da jirgin saman Lekan Asiri zuwa Najeriya.

Jirgin kamar yanda me saka ido akan ayyukan masu ikirarin Jìhàdì a yankunan Sahel, Brant Philip ya bayyana, yace ya yi leken Asirin ne a Jihar Borno, Akan Kungiyar ÌSWÀP.

Jirgin ya taso ne daga matsugunin kasar Amurkar dake kasar Ghana.

Sahara Reporters ta ruwaito Brant Philip yana cewa Gwamnatin Najeriya ta amincewa kasar Amurkar ta kai hari kan ‘yan kungiyar.

Sannan yace Amurkar zata yi amfani da jihar Naija a matsayin matsuguninta yayin wannan aiki.

Saidai hadimin tsohon shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya soki Brant Philip inda yace bai kamata ya fitar da wannan bayani ba dan bayanine na sirri kuma kamar yana ankarar da ‘yan Kungiyar ÌŚWÀP dinne su shiryawa harin.

Karanta Wannan  Yanzu da wata kungiyar Addinin Musulunci zata ce bata yadda da bada hutun Kirsimeti ba da ya zaka ji? Tsohon Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad inda yace bai kamata kungiyar Kiristoci ta CAN ta soki hutun da jihohin Arewa suka bayar a makarantu ba saboda watan Ramadana

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *