
A dazu ne hutudole ya kawo muku rahoton yanda wasu Kiristoci dalibai daga jami’o’in BUK, Kano da Kashere, Gombe inda suke zargin an hanasu gina coci a wadannan makarantu yayin da aka bar musulmai suka gina masallatai.
A martani ga wannan zargi shima wani dalibi musulmi yai zargin cewa an hana dalibai musulmai gina masallaci a jami’ar UNIJos, dake jihar Filato.
Yace duk da akwai masalacin da aka fara ginawa amma an hana a karasashi.
Sannan yayi zargin cewa an ma hana musulmai yin salla a masallacin da ba’a karasa ba.