Friday, December 5
Shadow

Yayin da akewa shugaba Tinubu matsin lamba kan ya sauke karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, Ministan zai tafi kasar Egypt dan halartar taro kan tsaro

Karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle zai tafi kasar Egypt dan halartar taro kan tsaro da ake gudanarwa.

Taron za’a yishi ne tsakanin ranar 1 zuwa 4 ga watan Disamba a birnin Cairo na kasar ta Egypt.

Taron yakan hada batun tsaro na Afrika da gabas ta tsakiya.

Hakan na zuwane bayan da kiraye-Kiraye suka yi yawa akan a sauke karamin Ministan bayan da babban Ministan, Muhammadu Abubakar Badaru ya sauka daga mukaminsa.

Karanta Wannan  YANZU-YANZU: Kakakin Majalisa Tajudeen Abbas Ya Janye Kudirin Tilasta Zaɓe wanda za'a rika cin mutum tarar Naira dubu dari bayan da ya sha suka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *