Friday, December 5
Shadow

Da Duminsa: Shugaba Tinubu ya aikawa majalisar Dattijai da sunan Janar Christopher Musa su tantanceshi a matsayin Minista tsaro

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya aika da sunan Janar Christopher Musa ga majalisar Dattijai dan su tantanceshi a matsayin ministan tsaro.

A cikin wasikar da shugaba Tinubu ya aikawa kakakin majalisar Dattijai Godswill Akpabio ya bayyana cewa yana son janar Christopher Musa ya maye gurbin Muhammad Abubakar Badaru a matsayin Ministan tsaro.

A jiya litinin ne dai Muhammad Badaru Abubakar ya ajiye mukaminsa a matsayin Ministan tsaro inda ya ce baya jin dadi.

Janar Christopher Musa na da shekaru 58 a Duniya kuma ya nuna bajinta a aikin soja sosai inda ya samu kyautukan karramawa da yawa.

Karanta Wannan  Na Yi Kewar Rashin Ganin Buhari Mai Gaskiya A Wannan Ziyara Da Na Kawo Jihar Katsina, Inji Shugaba Tinubu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *