
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, Najeriya zata fara kera sassan jirgin sama.
Shugaban ta bayyana hakane a wajan wani taro da aka gudanar kan jiragen sama na kasa da kasa a Najeriya.
Sakataren Gwamnati, George Akume ne da ya wakilci shugaban kasar a wajan taron ya bayyana haka.
Ya bayyana cewa kudin shigar Najeriya daga bangaren harkokin jiragen sama zasu kai Dala biliyan $2.56 nan da shekarar 2029.