Friday, December 5
Shadow

Fàdàn cacar Baki ya barke tsakanin Hausawa Musulmai ‘yan Arewa da Inyamurai a kafafen sada zumunta inda Hausawa suka fara mayar da martani kan shaguben da akewa ‘yan Arewa na cewa Inyamurai su koyi Hausa saboda ko da Tshàgyèràn Dhàjì sun kamasu

A baya hutudole ya kawo muku rahoton cewa, Inyamurai na koyon Hausa wai da tunanin idan ‘yan Bindiga suka kamasu suka musu Hausa, zasu sakesu.

Duk da yake abin ya zama kamar barkwanci amma da yawan Hausawa sun daukeshi a matsayj cin fuska da tsangwama da nuna cewa ‘yan Bindiga masu garkuwa da mutane ana musu kallon Hausawa ne.

Wannan dalili yasa Hausawa daga Arewa suma suka kafara mayar da martani ta hanyar dora wakokin Inyamurai suna bi a kafafen sada zumunta suna cewa idan masu son kafa kasar Biafra sun kamaka, kana yi musu wannan taken shikenan.

Wasu kuma sun rika cewa wai masu tsafi da iyayensu sune suke zagin Hausawa?

Karanta Wannan  Jadawalin masu kudin da suka bayar da tallafi ga wanda ambaliyar ruwa ta shafa a Jihar Borno

Hakan yasa suma Inyamuran abin bai musu dadi ba inda suka fara mayar da martani.

Kalli Bidiyon a comment:

@maina_uthman

Na to start to dey learn igbo remain 😂😂 #maina_uthman

♬ original sound – Sweet_shasha 💛

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *