
Bayan Tambayoyi da dambarwa, Majalisar Dattijai ta amince da Janar Christopher Musa a matsayin Ministan tsaro.
Hakan na zuwane bayan da aka kammala tantanceshi kuma sanatocin suka gamsu da irin amsoshin da ya basu.
Janar Christopher Musa zai fuskanci kalubale sosai a matsayin ministan tsaro duba da irin matsalolin tsaron da ake fama dasu a sassa daban-daban na kasarnan.