
Kakakin majalisar Dattijai, Godswill Akpabio ya koka da cewa, Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya matsa musu.
Ya bayyana hakane yayin tantance Janar Christopher Musa a matsayin sabon Ministan tsaron Najeriya.
Ya fadi cewa ya kamata a tambayi Janar Christopher Musa wane irin martani zai baiwa Shugaban Amurkar.
Akpabio ya bayyana hakane yayin da aka bukaci cewa a kyale janar Christopher Musa ya wuce ba tare da an masa tambayoyi ba.