Kakakin majalisar tarayya, Godswill Akpabio ya bayyana cewa, da tuntuni da sabon taken Najeriya ake amfani, da ba’a yi fama da matsalar ‘yan Bindigar da ake fama da ita ba.
Ya bayyana hakane a wata ziyara da ya kai wata tsangayar karatun Dimokradiyya a Abuja ranar Talata.
Ya kara da cewa saboda idan aka lura da taken yana sawa mutum soyayyar makwabcinsa wanda idan mutum na son makwabcinsa ba zai cutar dashi ba.
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya canja taken Najeriya daga wanda aka sani zuwa wannan sabon wanda ya jawo cece-kuce sosai.