
Rahotanni daga jihar Borno na cewa kananan yara 4 ne suka rigamu gidan gaskiya bayan fashewar Bàm a garin Banki dake karamar hukumar Bama a jihar ta Borno.
Kakakin ‘yansandan jihar,Nahum Daso ne ya tabbatar da hakan inda yace bam din ya tashine a tashar motar dake garin.
Yace yaran na wasa sa Bam dinne bayan sun daukoshi daga daji kamin ya fashe dasu.
Yace yaran da lamarin ya rutsa dash sune kamar haka:
Awana Mustapha, 15; Malum Modu, 14; Lawan Ibrahim, 12 da Modu Abacha, 12.