
Wasu iyaye na zargin wani malami da yiwa ‘ya’yansu 9 Luwadi a Abuja.
Lamarin kamar yanda gidan Rediyo da TV na Brekete Family suka ruwaito ya farune a Abuja inda iyayen har sun kai korafi wajan ‘yansanda kuma har an kama wanda ake zargi.
Saidai sun ce daga baya sun samu Rahoton cewa an sakeshi.
Mutumin an ce har jan Sallah yana yi a unguwarsu sannan kuma yaran sun ce idan yayi Luwadi dasu yakan musu barazanar Mutuwa idan suka gayawa wani.