
Jirgin sama na rundunar sojojin sama ta Najeriya yayi hadari a jihar Naija.
Jirgin ya tashi ne a sansanin sojin dake Kainji inda jim kadan da tashinsa ya samu matsala.
Jirgin na daukene da sojojin sama biyu amma sun samu damar ficewa daga ciki kamin ya fadi.
shugaban sojin saman Najeriya, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke ya jinjinawa kokarin da sojojin suka yi na karkatar da jirgin bai fada kan mutane ba.
Yace sojojin na cikin koshin lafiya kuma ana kara duba lafiyarsu.