
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa, Kano da Legas ne zasu fi amfana da Naira Biliyan 100 da ya ware na tallafawa harkar Ilimi.
Yace dalili shine wadannan jihohi sun fi sauran Jihohin Najeriya yawan Al’umma.
Yace zasu raba kudadenne zuwa kowacw karamar hukuma kuma zasu tabbatar kowace Karamar hukuma ta samu kudin daidai wadaida.