Ana kamuwa da ciwon hantane ta hanyar abinda ake cewa Virus, saidai wasu kalolin abinci, irin su giya, shan maganin gargajiya, da shan hadin gambizar magungunan asibiti ba tare da umarnin likita ba suma suna kawo cutar hanta.
Shan abubuwan zaki na leda ko na roba wanda aka sarrafa suma suna iya haifar da cutar hanta.
Hakanan yawan cin soyayyen abinci shima na iya haifar da cutar hanta.
Hakanan wasu ana haihuwarsu da cutar ta hanta.
Wannan virus na cutar hanta na yaduwa ne ta hanyar maniyyi, ruwa, abinci marar kyau, yin ma’amala ta kusa da wanda ya kamu ko ta hanyar jini.
Saidai ita wannan cuta idan bata yi tsanani ba ana iya warkewa.
Kuma akwai hanyoyi da ake bi wanda idan Allah ake inganta lafiyar hantar.
Allah ya karemu da lafiya. Amin.