
Rahotanni sun bayyana cewa, Hukumar yaki da rashawa da cin hanci, EFCC sun kulle gidan tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami inda matarsa, diyar tsohon shugaban kasa, Fatima Buhari take.
Jam’iyyar ADC ce ta bayyana hakan inda ta zargi Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da wulakanta Buhari ta wannan hanya.
Ana zargin Malami da Almundahanar kudade da yawa ciki hadda kudaden Abacha da aka kwato daga kasashen waje.