Kotun dake kula da cin zarafin mata da rikicin cikin gida dake Ikeja jihar Legas ta yiwa wani malamin Islamiya daurin rai da rai bayan samunsa da laifin yiwa dalibarsa me shekaru fyade.
Malamin me suna Alani Rafiu ya kai yarinyar masallaci inda ya mata fyade kuma ba sau daya ba sannan ya bata kudi dan kada ta gayawa kowa.
Mai Shari’a, Justice Rahman Oshodi ya bayyana cewa, malamin ya ci amanar iyayen yarinyar da suka amince dashi suka kaita wajanshi dan ya koyar da ita.
Sannan ya bata mata rayuwa a lokacin da ya kamata ace hankalinta na kan karatune.
Dan haka ya yanke masa daurin rai da rai sannan yace za’a saka sunansa a cikin rijistar masu fyade na jihar.