
Wata matar aure me ciki ta dauki hankula bayan data nemi mijinta ya je makwabta ya roko mata shinkafa da fa duka da suka dafa.
An ga matar rike da kwano a wani Bidiyo da ya watsu sosai inda tacewa mijin nata ya shiga Makwabta ya roko mata shinkafar saboda tana son ci.
Saidai mijin yaki, yace ta je da kanta ta roko da kanta.
Ya nuna Tuwon da ya dafa a gidan inda yace me yasa ba zata ci ba?
Lamarin dai ya jawo muhawara me zafi.

