Tuesday, December 23
Shadow

Kalli Bidiyon: A yayin da ya rage saura kwanaki 2 a tashi Duniya kamar yanda faston kasar Ghana yace, Mabiyansa da suka yadda dashi sun sayar da kadarorinsu sun koma wajansa da zama

Faston nan na kasar Ghana da ya ce wai an masa Wahayi Duniya zata tashi ranar Kirsimeti watau 25 ga watan Disamba kuma wai an ce masa ya kera jiragen ruwa 8 dan ya kwashi mutane a ciki saboda za’a yi ruwa irin na Dufana a yanzu ya fito yanawa mabiyansa bankwana.

Rahotanni sun ce wadanda suka yadda dashi tuni suka sayar da kadarorinsu suka koma wajansa da zama inda suke jiran ranar 25 ga wata tazo.

An ganshi ya fito yanawa mabiyan nasa bankwana.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Baturiya 'yar kasar Amurka ta Bar Kiristanci ta musulunta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *