
Rahotanni sun bayyana cewa tun a watan Nuwamba, kasar Amirka na ta tattara bayanan sirri akan Najeriya.
Rahoton yace an gano hakanne ta hanyar amfani da na’urar dake bibiyar jiragen sama.
Kafar Reuters ce ta ruwaito wannan labari.
Labarin na zuwane yayin da kasar Amurka tace ba zata yi amfani da karfin soji ba a Najeriya dan taimakon Kiristoci da aka ce ana kashewa.