
Kakakin Majalisar Dattijai, Godswill Akpabio ya bayyana cewa tankar dakon man fetur ta yi taho mu gama da daya daga cikin motocin dake tawagarsa.
Lamarin ya farune a Ibadan jihar Oyo ranar Lahadi, kamar yanda Akpabio ya sanar a zaman majalisar.
Yace daya daga cikin ‘yansandan dake masa rakiya, Ibrahim Hussain ya rigamu gidan gaskiya kuma har an binneshi.