
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, sun tuntubi kasar Turkiyya dan ta taimakawa Najeriya wajan magance matsalar tsaro.
Ya bayyana hakane yayin ganawa da kungiyar Kiristoci ta CAN a ziyarar data kai masa a fadarsa dake Abuja.
Shugaban yace akwai bukatar Kiristoci su taya Najeriya da Addu’a dan kawo karshen matsalar.
Ya kuma kara da cewa, sun siyi Jiragen yaki 3 daga kasar Amurka amma ba zasu zo da wuri ba.
Hakan na zuwane bayan da Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya baiwa Gwamnatin tarayya shawarar ta yi watsi da kasar Amurka ta koma neman taimakon tsaro daga kasashen China, Pakistan da Turkiyya.